(ABNA24.com) Wadannan kalamman sun fito ne a bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Chinar, Zhao Lijian, bayan da shugaba Trump, na Amurka, ya baiwa caccaki hukumar lafiya ta duniya da kuma zarginta da cewa ‘yar amshin shatan China ce.
M. Zhao, ya bukaci Amurka, ta daina dora laifi kan kasarsa, hasali ma ta maida hankali kan yaki da annobar korona, data kashe mutum 90,000 da kuma kama sama miliyan 1,5 a kasar ta Amurka.
Shi dai shugaba Trump ya bayyana cewa bai ji dadin aikin hukumar ta WHO ba, inda ya dibar wa hukumar wa'adin kwanaki talatin na ta gyara inda ya ce idan har al'amura ba su daidaita ba to zai daina bai wa hukumar tallafi baki daya kuma Amurka za ta fice daga Hukumar.
Amurka dai ita ce kasar dake kan gaba nesa ba kusa ba, wajen samar wa da hukumar lafiya ta duniya tallafin kudi.
/129
20 Mayu 2020 - 07:18
Lambar labari: 1038603
Kasar China, ta ce Amurka na neman bata mata sunane a idon duniya, saboda a cewarta Amurkar ta kasa shawo kan annobar korona da ke damun ta.